24 Satumba 2020 - 11:15
Mali:Mai Yuwa ECOWAS Ta Dage Takunkuman Tattalin Arzikin Da Ta Dorawa Kasar Gobe Jumma'a

Ana saran kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS zata dagewa kasar Mali takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 18 ga watan Augustan da ya gabata.

Shafin yanar gizo na Labara Africa News ya nakalto jakadan kungiyar na musamman a kasar ta Mali Dr GoodLuck Jonathan tsohon shugaban kasar Najeriya yana fadar haka a lokacinda ya je kasar ta mali don ganewa idaninsa irin ci gaban da aka samu.

Kafin haka dai sabon shugaban kasar da aka zaba Kanar Bah Ndaw, dan shekara 70 wanda kuma shi ne ministan harkokin tsaron gwamnatin da ta shude, ya bukaci kungiyar ta dagewa kasar takunkumin da aka dorawa kasrsas.

A Gobe jumma’a ne ake saran za’a rantsar da shugana kasar da kuma mataimainsa a gwamnatin watanni 18 da zasu fara jagoranta.

342/